Makomar sulhu tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
February 14, 2012Ana fuskantar kwan gaba kwan baya, a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu a birnin Adis Ababa na ƙasar Ethiopiya.A makon da ya gabata ɓangarorin biyu sun cimma nasara rattaba hannu kan yarjejeniyar daina kaiwa junan hari, to amma a cewar ministan harakokin wajen Sudan ta Kudu , hukumomin Khartum har sun karya wannan yarjejeniya kwana ɗaya rak bayan rattaba mata hannu.
Tabon Mbeki tsofan shugaban ƙasar Afrika ta Kudu da ke cikin tawagar masu shiga tsakanin ƙasashen biyu, ya ce duk da haka an samu babban ci gaba ta fannin zaman lafiya a yanki ya kuma bada hujja:Taron ya amince da girka rundunar haɗin gwiwa, wadda za ta sa ido kan iyakokin ƙasashen biyu domin tabbatar da yarjejeniyar da su ka cimma.
Saidai har yanzu ba a samu daidaituwa ba, game da taƙƙadamar man fetur.
Sudan ta Kudu wadda ta mallaki kashi uku cikin hudu na wannan albarkar ƙarƙashin ƙasa,ta rufe rijiyoyin man har sai an cimma yarjejeniya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Mohammad Nasiru Awal