1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta ba wa Nijar kudin yakar ta'addanci

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
July 18, 2022

Jamhuriyar Nijar za ta ci moriyar euro miliyan 25 a matsayin tallafi daga kungiyar EU, a kokarinta na kara inganta harkokin tsaro musamman yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4EIbC
Mahamadou Issoufou und Alexander De Croo
Hoto: Nicolas Maeterlinck/BELGA/dpa/picture alliance

Burin da fadar mulki ta Niamey ke son cimma wa da kudin shi ne na karfafa dakarun tsaro ta fannoni da dama, ciki har da kwarin gwiwar jajircewa a fagen daga da kare fararen hula.

Ita dai kungiyar ta EU da ke dasawa da Nijar, ta ce za ta gina wani sansanin soja a yankin Tillaberi da ke yammacin kasar, da kuma kafa wata cibiyar horas da jami'an tsaro makamar aiki.

Jamhuriyar Nijhar ta zama kasar da Faransa ta dogara a kanta a yankin Sahel, tun bayan da Mali ta bukaci sojanta su kwashe nasu-ya-nasu su fice daga kasar bayan shafe fiye da shekaru tara suna yaki da ta'addanci.