Malamai sun bijire wa jami'o'in isra'ila
October 27, 2015Wasu kwararrun malaman jami'a kimanin 340 masu koyarwa a jami'o'i sama da 70 na kasar isra'ila sun bada sanarwar shirin raba gari da jami'o'in kasar ta Isra'ila dama kaurace wa duk wasu tarurrukan da jami'o'in za su shirya ko za su dauki dawainiyar shiryasu a nan gaba.
Malaman wadanda suka bayyana wannan matsayi nasu a cikin wata budaddiyar wasika da suka wallafa a wannan Talata a cikin jaridar The Guardian mai fita kullun sun ce sun yi haka ne domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira yawaitar take hakin dan Adam da Isra'ilar ke yi wa daukacin al'ummar Palasdinawa.
Daga cikin masanan da suka bada goyan bayansu ga shirin raba gari da jami'o'in kasar ta Isra'ila wasunsu sun fito daga wasu fitattun jami'o'in Birtaniya kamar su Oxford da Cambridje.