Malaysia ta gargadi mamallakan Facebook da TikTok
April 9, 2024Malaysia ta bukaci mamallakin kamfanin Meta da ke da shafin Facebook da kuma mai kamfanin TikTok da su kara azama wajen sanya ido kan miyagun ta'adun da ake yadawa ta shafukansu, sakamakon korafe-korafen da ta karba masu yawa na karuwar miyagun dabi'u a shafukan na sada zumunta na zamani.
Karin bayani:An harbo wani jirgin saman fasinjan Malaysia a gabashin Ukraine
A wata sanarwar hadin gwiwa da rundunar 'yan sandan kasar ta fitar, ta ce a cikin watanni ukun farkon wannan shekara kadai, ta karbi korafe-korafe 51,638 game da Meta da TikTok, sannan kuma a bara korafe-korafe 42,904 aka shigar mata.
Karin bayani:Kotu ta sami Najib Razak da Almundahana
A cikin watanni shidan farko na shekarar 2023 da ta gabata, kamfanonin Meta da TikTok sun toshe wallafe-wallafe da dama da masu ta'ammali da shafukan suka yi a Malaysia.