Bamako: 'Yan adawa da masu mulki sun tattauna
June 8, 2018Talla
Yayin wannan zaman taro da ke zuwa kasa da watannin biyu kafin zaben shugaban kasar ta Mali, Firaministan Soumeylou Boubeye Maïga, ya sha alwashin ci gaba da tuntubar 'yan adawa da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an gunadar da zabukan kasar cikin kyakkyawan yanayi da amincewar kowa.
Yayin da Firaministan ya ce tattaunawar ta su da 'yan adawa ta gudana cikin kyakkyawan yanayi, a hannu daya kuma Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai, da kuma Amirka, nuna fargabarsu suka yi dangane da tashe-tashen hankulan da aka fuskanta tsakanin bangarori biyu na 'yan siyasar kasar Mali a ranar biyu ga watan Yuni.