1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manafort zai bai wa kotun Amirka hadin kai

Mouhamadou Awal Balarabe
September 14, 2018

Tsohon shugaban yakin neman zaben Donald Trump ya amsa laifin da Kotun Amirka ke tuhumarsa da aikatawa tare da yin alkawarin bayar da hadin kai dangane da bincike kan Rasha.

https://p.dw.com/p/34tRo
USA - Ermittlungen zur Russland-Affäre - Paul Manafort
Hoto: picture alliance/AP/P. Martinez Monsivais

Tsohon darektan yakin neman zaben shugaban Amirka Donald Trump wato Paul Manafort ya amince da laifin da kotu ke tuhumarsa da aikata na hada kai da wasu don cin amanar kasarsa, kuma ya yarda da yin aiki da mai gabatar da kara Robert Mueller a kan binciken zargin Rasha kan kutsen zabe.

Manafort mai shekaru 69 da haihuwa ya rigaya ya amince tun a watan Agusta da laifin zambatar baki cikin aminci da kin biyan haraji a wata shari'a da ta gudana a jihar Virginia. Wannan mika wuya na tsohon mai dasawa da shugaban na Amirka zai sa ya kauce wa hukuncin mai tsanani, wanda kuma ka iya shafa wa Trump kashin kaji makonni kalilan kafin zaben 'yan majalisa na tsakiyar wa'adinsa na mulki.

Fadar mulki ta White House ta yi gaggawar tabbatar da cewa shawarar da Paul Manafort ya yanke ba ta da nasaba da "shugaban Amirka da kuma yakin neman zabe da ya ba shi nasara a shekarar 2016". Dama shugaba Trump ya fada cewa ana tuhumar Manafort ne domin yi masa bita da kullin siyasa.