Bayern ta kammala daukar Mane
June 22, 2022Talla
Dan wasan gaba na aksar Senegal Sadio Mane ya sa hannu kan kwantiragin shekaru na taka leda a Bayern kan kudi kusan Yuro miliyan 40, sai dai Mane na da sauran shekara daya na murza leda a Liverpool.
Dan wasan mai shekaru 30 ya bar Anfield bayan buga wasanni 269, inda ya zura kwallaye 120 a dukkan wasannin da ya buga, wanda hakan ya taimaka wa kungiyar ta lashe gasar zakarun Turai a kakar wasa ta 2018-19 da kuma gasar Premier bayan kaka daya.
Dan wasan ya zama dan wasa na uku da Bayern ta dauko a karshen kakar wasa ta bana, bayan zuwan 'yan wasan Ajax Amsterdam Ryan Gravenberch da Noussair Mazrouai.