Manufar Jamus dangane da yaki a ketare
February 3, 2014Amirka da kuma kasashen Turai da ke kawance da Jamus, sun yi marhabin lale da alkawarin da mahukunta a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus suka yi, na kara taka rawa ta fuskar manufofin ketare da na tsaro, amma kuma ba tare da wani kudiri na tura dakaru domin yaki ba. Wannan dai na nufin kara bayar da tallafi a fannin bayar da horo da kuma kayayyakin aiki.
A cikin sakonsa ga babban taron kasa da kasa akan sha'anin tsaro a birnin Munich na nan Jamus, shugaban Jamus Joachim Gauck ya bayyana cewar, a kokarin da Jamus ke yi na kasancewa kyakkyawar abokiyar kawance, za ta kara taka rawar gani a harkokin da suka shafi ketare, kalaman da kuma ministocin kula da harkokin ketare da na tsaron Jamus suka jaddada a wajen taron.
Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya ce Jamus fa, babbar kasa ce da ta wuce matsayin yin tsokaci a kan harokin siyasar ketare - ta bayan fage kadai. Sai dai kuma adawa da tura dakarun Jamus domin yaki a ketare, za ta sa kudirin da jami'an suka bayyana ya yi matukar wahala.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal