Manyan sojoji na murabus a Sudan ta Kudu
February 17, 2017Wani minista a gwamnatin Sudan ta Kudu ya koma bangaren 'yan adawa kamar yadda wata wasika da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya karanta a ranar Juma'ar nan ta nunar. Wannan dai shi ne karo na biyu da wani babban jami'i daga bangaren gwamnatin ta Sudan ta Kudu ya sauka daga kujerarsa a wannan kasa da tuni yaki ya tagayyarata.
Lutanal Janar Gabriel Duop Nam da ke zama ministan kwadago a kasar ya mika takardar sauka daga mukamin nasa inda ya ce ya yi mubayi'a ga bangaren mataimakin shugaban kasa Riek Machar.
Kwanaki shida dai kenan wani babban sojan kasar ta Sudan ta Kudu Lutanal Janar Thomas Cirillo Swaka, ya bayyana ajiye kakinsa, sai dai a nasa bangaren bai bayyana munbayi'a da bangaren na 'yan tawaye ba, sai dai ya zargi mahukunta na kasar da kokari na mayar da rundinar sojan kasar ta wata kabila guda daya da ma goyon bayan aiyukan cin zarafi da sojan kasar ke wa wata kabila.