Cimma yarjejeniyar huldar diplomasiyya
December 11, 2020Talla
Marokon ta bi sawun Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Sudan, a matsayin wadanda za su ci gaba da alaka da Isra'ila, wanda ake gani yunkurin Amirka ne na yin taron dangin yakar Iran ta hanyar rage kaifin tasirinta a yankin Gabas ta Tsakiya.
A wani yunkuri na sauya matsayin Amirka, bisa ga yarjejeniyar shugaba Donald Trump ya amince da la'akari da cewar Maroko ce ke da 'yancin mallakar yankin yammacin Sahara, yankin da ke cikin rikici na gomman shekaru tsakanin Marokon da mayakan Polisario da ke da goyon bayan Aljeriya, wadanda kuma ke fafutukar neman 'yancin cin gashin kai.