Martani kan dokar haramta taro a Yuganda
August 7, 2013Dokar wadda aka zartar da ita ranar Talata, na haramta duk wani taro ko gangami da ya shige mutane uku. Sabuwar dokar dai na kara wa 'yan sanda karfin iko na amfani da kowane irin mataki na tarwatsa taron mutane fiye da uku da hukuma bata amince dashi ba. Rahotanni daga Ugandan dai na nuni da cewar, 'yan sandan ƙasar ba sa darajawa 'yan adawa, abin da ke tabbatar da cewar wannan doka tamkar gasa musu tsakuwa a tafin hannu ne.
Da ya ke yin tsokaci a madadin gwamnati, mataimakin shugaban kwamitin da ke kula da harkokin yau da kullum a majalisar ƙasar, kuma dan jam'iyyar da ke mulki ta NRM, Moses Ali ya jaddada cewar dokar za ta kare 'yancin al'umma.
Sai dai Sarah Jackson da ke zama mataimakiyar direktan da ke kula da shiyyar Afirka ta ƙungiyar kare hakkin jam'a ta Amnesty International, ta ce wannan dokar tamkar cin zarafin ne.
Kamar dai mafi yawan masu suka, ita ma Sarah Jackson na ganin rashin dacewar wannan doka, domin razana 'yan adawa tare da kare gwamnatin shugaba Yoweri Museveni, wadda ta jima tana fuskantar mummunar zanga-zangar ƙin jinin gwamnati dangane da tsadar rayuwa da cin hanci da rashawa da kuma take hakkin bil'adama a kasar.
Peter Basigye direktan gudanarwa ne a cibiyar lura da harkokin yada labarai a Afirka, reshen Kamfala wanda ya yi tsokaci dangane da dalilan kafa wannan doka.
Ya ce" gwamnati tana da rinjaye a majalisa, a yayin da a hannu guda kuma akwai 'yan adawa da ƙungiyoyin jama'a da na kare hakkin bil'adama, ya zamanto wajibi a ɓangaren gwamnati ta ɗauki matakin da suka cancanta dangane da 'yancin faɗin albarkacin baki".
Dokar dai na nufin cewar duk wani gangami ko taro na lumana da ya kunshi yawan mutane kama daga uku, zai zame mummunan laifi. Hakan na nufin cewar duk wani gangami na siyasa daga yanzu a Uganda na fuskantar barazana, domin jami'an tsaro za su iya amfani da bakin bindiga a kan masu wucewa a gefen taron ko kuma su mahalarta taron. Sai dai Peter Basigye ya ce baya ganin 'yan adawa da ma al'ummar Yuganda za su razana da wannan dokar.
" Ina ganin a wannan ƙasar mun kai wani matsayi da doka kadai ba za ta iya yin tasiri ga mutanen da ba su amince da abin da gwamnati ta ke yi ba. Don haka ƙungiyoyin kare hakkin jama'a da 'yan adaw za su ci gaba da fafutukarsu, ko 'yan sanda sun ba su izini ko kuma a'a".
A martaninsa game da dokar dai, shugaban n adawa a majalisar Yuganda, Nandala Mafabi ya ce , dokar ta sabada tsarin mulki, kuma zasu kalubalance ta a kotun tsarin mulkin kasar.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdurrahman Hassane