Sudan za ta amfana da hulda da Isra'ila inji masana
October 26, 2020Masana a yankin Gabas ta Tsakiya sun ce yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin Isra'ila da Sudan aba ce da za ta amfani kasashen biyu har ma da Amirka da shugabanta Donald Trump wanda shi ne ya shiga tsakani a aka kai ga cimma matsayar. Sai dai masu sharhi kan lamuran a yankin na ganin lamarin ka iya kasancewa mai sarkakiya ga kasar ta Sudan nan gaba.
Watanni biyun da suka gabata ne aka sanya danba ta daidaita lamura tsakanin Sudan da Isra'ila bayan wata ziyara da Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya kai yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan ziyara har wa yau ta share fage na daidatuwar lamura tsakanin Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, batun da masu sanya idanu kan harkokin da ka je su koma yankin gabas ta tsakiya ke maraba da shi, sai dai kuma a share guda wasu na ganin wannan kamar an yi gaggawa wajen daidaita komai.
Wani abu har wayau da ke cigaba da jan hankalin 'yan Sudan din da ma masharhanta shi ne kudin da kasar za ta biya na diyya kan hare-haren ta'addancin, inda Shugaba Trump na Amirka ya ce kafin kasarsa ta janye takunkumi da ta kakaba wa Sudan din kamar yadda aka yi alkawarin yi bayan da suka daidaita da Isra'ila, sai mahukuntan Khartoum sun biya tsabar kudi dala miliyan 335 don bayarwa a matsayin diya ga wadanda harin ta'addanci ya shafa ofisoshin jakadancin Amirka da ke Nairobin Kenya da Dar es Salam a Tanzaniya wanda Osama Bin Laden ya kai a lokacin da yake zaune a Sudan. Da yake tsokaci kan wannan batu, Kristian Brakel na cibiyar hulda da kasashen ketar da ke nan Jamus ya ce muddin Sudan za ta samu abinda take so wadannan kudade da ake so ta bada ba a bakin komai suke ba duk kuwa da cewar kasar ba ta da kudi sosai.
Yanzu haka dai da dama na cigaba da zuba idanu don ganin yadda lamura za su mika tsakanin Sudan da Isra'ila da ma sauran makotanta da ke gabas ta tsakiya a daidai wannan loakci da Khartoum ta bude wani sabon babi na kawance da Isra'ila wadda ta jima suna zaman 'yan marina da ita.