1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Martani kan hasashen yunwa a 2023

January 17, 2023

Hukumar samar da abinci da ayyukan gona ta duniya FAO ta ce ‘yan Najeriya kimanin miliyan 25 na fuskantar barazanar matsanaciyar yunwa a shekarar 2023, kari kan adadin da ake da su yanzu.

https://p.dw.com/p/4MKq9
Nigeria Landwirtschaft Bauern
Hoto: Ifiok Ettang/AFP

Dama dai kungiyar abincin ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta yi hasashen za a samu karuwar masu fama da yunwa kimanin miliyan 17 a shekarar da ta gabata inda kuma a wannan shekarar ta yi hasashen cewa alkaluman za su karu zuwa mutum miliyan 25.

Kungiyar FAO ta danganta karuwar yunwa a Najeriya da matsaololin dumamar yanayi da rashin tsaro da tsadar abinci gami da rashin ingantattun manufofin habaka noma daga hukumomi.

Tuni dai masana da masharhanta da kuma talakawa suka fara tofa albarkacin bakin su kan wannan rahoto na samun karuwar yunwa tsakanin ‘yan kasar inda su ke bayyana damuwa na halin da za shiga tare da bada shawarwarin abin da ya kamata a yi.

Kwamared Bishir Dauda sakataren kungiyar muryar talaka ta kasa ya ce rahoton ya kara fito da fargabar da ake da ita na halin da ake ciki a kasar.

Masanan sun kuma bada shawarar abin da ya kamata a yi a wannan yanayi da aka samu kai a ciki na rashin abinci wanda aka yi hasashen zai iya haifar da yunwa mai tsanani a kasar da ke fama da matsaloli daban-daban.

Sai dai masu rajin kare hakki muhalli kamar Abdullahi Muhammad Inuwa na ganin matukar ba a magance matsalolin dumamar yanayi ba duk matakan da aka dauka kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.

Hukumomi a Najeriya dai na ikirarin daukar matakai na inganta noma da kiwo ta yadda za a karfafa samar da abinci da yaki da yunwa sai dai da dama na ganin matakan ba sa yin tasiri saboda rashin aiwatarwa da kuma sa ido inda siyasa ke shiriritar da wasu manufofin da dama.