1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Mataki kan hari a Saudiyya

Gazali Abdou Tasawa
September 16, 2019

Amirka ta ce a shirye take ta mayar da martani kan kasar da ke da alhakin kai hare-hare da jirage marasa matuka, a cibiyoyin hakar man fetur din Saudiyya.

https://p.dw.com/p/3PeaL
Saudi-Arabien Drohnenangriffe
Hoto: Reuters

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twiter, Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce suna kyautata zaton sun san wanda ke da alhakin kai wadannan hare-hare, amma suna jiran Saudiyyar ta bayyana musu wanda take zargi da kuma irin matakin sojan da take son ganin Amirkan ta dauka.

 Wannan dai shi ne karo na farko da Shugaba Trump ke bayyana yiwuwar daukar matakin soja a cikin wannan rikici. Kungiyar 'yan tawayen Shi'a ta Houthis ta kasar Yemen ce dai ta dauki alhakin wadannan hare-hare.

 Sai dai Sakataren harakokin wajen Amirka Mike Pompeo ya zargi kasar Iran da kaisu, zargin da mahukuntan Tehran suka yi watsi da shi suna masu cewa Amirkar na neman wata kafa ce kawai ta kafa hujjar kai musu farmaki.