Amnesty ta soki rusa gine-gine a Abuja
August 25, 2022Wannan matsala ta rushe-rushen gidaje, shaguna da ma sauran gine-gine a Abuja hedikwatar Najeriyar da hukumar kula da babban birnin ke yi a yanzu ta shafi unguwanni da dama da ke cikin gari da ma gefen Abuja inda hukumar ta bayyana rusa sama da gine-gine 400. Wannan ya shafi daukacin kananan hukumomin birnin, na baya baya nan shi ne wanda ta yi a unguwar Durumi ta uku inda hukumar ta rusa gine-gine da dama.
Wannan ya sanya hukumar kare hakin jama'a ta Amnesty International shiga cikin lamarin inda ta ce matakin da hukumar ke dauka ya wuce iyaka domin ya shafi batu na hakkokinsu a matsayinsu na ‘yan Najeriya, wannan ya sanya ta yi tattaki zuwa unguwar don yi wa ‘yan jaridu bayanin matsayinsu a kan wannan.
Akwai dai magidanta da suka bayyana cewa fiye da shekaru 50 suna zaune a wannan unguwa sune ma asalin mazaunan Abuja. To sai dai hukumar kula da birnin Abuja ta ce tana rushe-rushen wuraren da suke maboyar bata gari da barayi da ma zargin ‘yan ta'adda na samun mafaka.
Amma ga Kungiyar Amnesty International din dai ta ce da sakel. Hukumar dai ta ce ba ja da baya a kan rushe-rushen da ta sanya a gaba domin tsabtace birnin daga gine-ginen da aka yi ba bisa kaida ba.