1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Hollande kan kisan Malamin Coci

Yusuf BalaJuly 26, 2016

Shugaba Hollande ya nuna fushinsa kan kisan da aka yi wa wani malamin majami'a a Faransa sanadiyar yankan rago da wani da ke da nasaba kungiyar IS ya yi masa.

https://p.dw.com/p/1JWES
Francois Hollande und Bernard Cazeneuve
Hoto: Reuters/P. Rossignol

Shugaba Francois Hollande na Faransa a ranar Talatan nan ya bayyana cewa mutane biyu da suka yi garkuwa da wani babban malamin coci a yankin Normandy a Arewacin Faransa 'yan ta'adda ne da suka yi mubayi'a da kungiyar 'yan ta'addar IS. Shugaba Hollande ya ce kungiyar ta IS ta kaddamar da yaki a kansu dan haka dole su tashi tsaye da bin duk wata hanya da ta dace da shari'ar wajen murkushe ayyukan 'yan ta'adda. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci majami'ar da ke garin Saint-Etienne-du-Rouvray a Kudancin Rouen.

Mai magana da yawun fadar Vatican Fadar Federico Lombardi ya bayyana abin da ya faru a matsayin labari mai tada hankali kuma Fafaroma Francis ya nuna alhininsa tare da jajanta wa al'ummar kasar da ma majami'ar. Tuni dai 'yan sandan kasar ta Faransa suka aika mayakan na IS lahira bayan da suka yi garkuwa da malamin kafin su kashe shi.