Martanin soke zaben Kenya
September 1, 2017Jagoran 'yan adawan kasar ta Kenya Raila Odinga, ya bayyana hukuncin da aka yi a matsayin wani ci gaban demokradiyar Afirka baki daya.
"Wannan babban tairihi ne ga al'ummar Kenya dama a fadin Afirka baki daya. A karon farko cikin tarihin demokradiyar Afirka, an samu hukuncin da ya soke zabe bisa kura-kurai da aka tabka a zaben shugaban kasa"
Tun da farko dai hukumar zaben kasar Kenya ta ayyana Shugaba Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zabe da ya gudanan ranar 08.08.2017, amma yan adawa suka ce da sakel. A lokacin kungiyoyin sa'ido kan zabe daga kasashen duniya, duk sun yaba da zaben kuma suka kwatanta shi a matsayin mai tsabta wanda aka yi bisa ka'ida.
Shugaba Kenyatta a martaninsa ya sanar da yin watsi da soke zaben da kotu ta yi, amma ya ce zai yi biyya ga hukunci don haka zai sake komawa fagen daga don neman jama'a.
Yanzu dai kotun kolin na kasar Kenya ya bada umarnin a gudanar da sabon zabe nan da kwanaki 60.