1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan NIjar kan ficewar AES daga ECOWAS

Gazali Abdou Tasawa
December 16, 2024

A Jamhuriyar Nijar Jama'a na tsokaci kan sakamakon taron kungiyar ECOWAS wanda ya amince da matakin kasashen Nijar Mali da Burkina Faso na AES na ficewa daga kungiyar ta ECOWAS

https://p.dw.com/p/4oDkz
Gangamin wasu yan kasar Nijar a birnin Yamai
Hoto: AFP/Getty Images

Kungiyoyin da ke goyon bayan mulkin soja da kuma sabuwar tafiyar da suka kira ta neman samun cikakken ‘yancin kan kasashen Sahel na a sahun gaban wadanda suka nuna farin cikinsu da matakin raba gari da kungiyar Ecowas wanda zai soma aiki daga ranar 29 ga watan Janairun 2025.. Sai dai wasu ‘yan Nijar din na kallon matakin karin wa'adin watanni shida kafin karkare shirin ficewar baki daya a matsayin wata dama ta sake shawo kan kasashen na AES kan su ci tuwon fashi. To amma Malam Bana Ibrahim na kungiyar Front Patrotique na ganin bakin alkalami ya rigaya ya bushe game da maganar ficewa daga ECOWAS.

Shugabannin kungiyar kasashen AES
Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Gare mu tafiya daga ECOWAS ta tabbata babu wata maganar mu dawo. Abin da muka sa a gaba shi ne mu zo mu tattauna da ECOWAS mu ga yadda zamu gudanar da sabuwar huldar da su don gyara zamantakewarmu. Ka san kafin ma a yi ECOWAs kasashenmu suna da hulda a tsakaninsu. To wannan ne zamu yi a tsawon wadannan watanni shidan nan da suka kebe"

To amma Malam Sahanin Mahamdou na daga cikin wadanda ke ganin wa'adin watannin shida wata dama ce ta sake zawarcin kasashen na AES kuma a cewarsa Nijar ita ce za ta fi sauran kasashen wahala idan matakin ficewar daga ECOWAS ya tabbata.

Taron shugabannin ECOWAS a Abuja, Najeriya
Hoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Ko shakka babu wata dubara ce ta diplomasiyya saboda a samu a gyara abun cikin ruwan sanyi. Saboda abin babban tasirin da za shi yi ba fa yanzu-yanzu ba ne. Sai a nan gaba ‘yan kasashenmu za su dandana kudarsu musamman wadanda suke kasashen waje kamar Cote d'Ivoire da Najeriya da Ghana da sauransu. Kuma kasar da za ta fi shan wahala da farko ita ce Nijar domin mu babbar kasar da muke hulda da ita ita ce Najeriya wacce huldarmu ta kasuwanci na da karfi sosai. Dan haka a gaba matsala tsakaninmu da Najeriy babbar barazana ce ga tattalin arzikin kasarmu 

Sai dai Malam Roufa'i Sani mai sharhi kan harkokin tsaro a Nijar ya ce ko ma me zai faru a tsakanin ECOWAS da AES akwai huldar da ba za ta sauya ba musamman a fannin tsaro.

Wasu yan kasar Nijar a birnin Yamai
Hoto: AFP

In ka dauki misali kamar Nijar da Najeriya, ko da Nijar ta fice daga cikin Ecowas, to ganin kalubalen da suke fuskanta tare a fannin tsaro tun daga yankin Tafkin Tchadi ya zuwa Kudancin kasar Nijar da Arewacin Najeriya  inda aka samu bullar sabuwar kungiyar ta'addanci ta LAKURAWA, dole ne wadannan kasashen sai sun yi aiki tare. Haka ma da Nijar da Benin ko kuma Mali da arewacin Cote d'Ivoire dole su yi aiki tare su kalubalanci matsalar tsaro 

Sai dai kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa za ta iya yin hulda da kasashen na AES dabam-dabam amma ba da sunan kungiyarsu ta AES ba.To ko wace fassara za a iya yi wa wannan mataki?

Abin jira a gani dai a nan gaba shi ne yadda hulda za ta kasance a tsakanin kasashen na ECOWAS da kuma takwarorinsu na AES bayan da zamansu tare na tsawon shekaru 50 ya kawo karshe.