Dakarun Masar sun hallaka shugaban IS a Sinai
August 5, 2016Talla
A cewar rundunar sojojin Masar din, sun hallaka al-Ansari ne tare da wasu 'yan ta'adda 45, yayin wasu jerin hare-hare da suka kai a maboyar 'yan ta'addan da ke kusa da Arish babban birnin gundumar arewacin Sinai din, kana kuma sun raunata wasu 'yan ta'adda 20. Sai dai har kawo yanzu babu tabbaci kan lokacin da dakarun yaki da ta'addancin na Masar suka kai hare-haren a yankin na Sinai da ke fama da ayyukan 'yan ta'adda.