Masar na taimaka wa Falasdinawa a Rafah
May 15, 2021Wata majiyar fannin kiwon lafiya ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa fadar mulki ta Alkahira ta bude hanyar Rafah, da ke zama kan iyaka daya tilo da Isra’ila ba ta killace ba don diban marasa lafiya na yankin Falasdinawa.
Rikicin da ke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu na ci gaba da ta’azzara kwanaki da dama bayan fara shi, inda sojojin Isra’ila suka fadada kai hare-hare a matsayin martani bayan harbe-harben rokoki da kasarsu ta fuskanta daga Zirin Gaza. A daren Jumma'a zuwa yau Asabar dai, sojiin na Isra'ila sun kashe wasu Falasdinawa 10 ‘yan gida daya, a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai.
Kasashen Larabawa da ke da kusanci da Isra'ila sun nuna damuwa dangane da wannan rikici. Hukumomin yankin Falasdinu sun ba da rahoton cewa wadanda suka mutu ya kai mutane 139 ciki har da yara 39, a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama tare kuma da yin ruwan bama-bamai a Zirin Gaza. A nata bangaren Isra'ila ta ce 'yan kasarta tara ne suka mutu, ciki har da wani yaro da kuma wani soja.