Masar ta soki Isra'ila kan dokar kasar Yahudawa
July 21, 2018Talla
Kasar Masar dai ta kasance kasar Larabawa ta farko da ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila a shekarar 1979 matakin da ya kawo karshen shekaru da dama na zaman doya da manja tsakanin kasashen. A cewar ma'aikatar harkokin wajen Masar bayyana kasar Isra'ila a matsayin kasar Yahudawa zalla zai haifar da wariya da yin zagon kasa ga shirin zaman lafiya da ake son kullawa a kasar.