Makusancin shugaban Amurka Jake Sullivan ya sauka a Isra'ila
December 14, 2023Yayin da dakarun sojin Isra'ila ke ci gaba da barin wuta a Gaza, mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya sauka a birnin Kudus yau, don ganawa da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Isra'ila Isaac Herzog game da yakin.
karin bayani:Gaza: Isra'ila ta mamaye asibitin Al-Shifa
Mr Netanyahu da ke fuskantar matsin lambar tsagaita wuta daga Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashen, ya sha alwashin ci gaba da yakin har sai ya kawar da duk wani burbushi na kungiyar Hamas da wasu kasashen yamma suka ayyana a matsayin ta ta'addanci.
karin bayani:Isra'ila ta yi asarar babban jami'in sojinta a Gaza
Hare-haren Alhamis din nan dai sun hallaka Falasdinawa 67, in ji ma'aikatar lafiya ta Gaza, adadin da ya kai Falasdinawa kusan dubu goma sha tara kenan da rikicin ya hallaka.