Maslaha ga rikicin Sudan da Sudan Ta Kudu
April 3, 2013A wannan Alhamis (04.04.2013) ne wa'adin janye dakaru daga kan iyakar da kasashen Sudan da Sudan Ta Kudu ke takaddama akai ke cika, sakamakon yarjejeniyar da sassan biyu suka sanyawa hannu domin kawo karshen fito na fiton da suka yi a baya. Sai dai duk da cewar ba a kai ga warware rikicin da ke tsakanin su baki daya ba, amma an sami ci gaba.
Tunma gabannin Sudan Ta Kudu ta sami 'yanci a shekara ta 2011, dukkan sassan biyu na yin ja-in-ja game da rabon kudaden da suke samu daga kasuwancin man fetur. Sulusin rijiyoyin man din a wancan lokacin suna yankunan da a yanzu ke karkashin Sudan Ta Kudu ne, amma kuma bututun da ke safarar man fetur din ya ratsa ne ta Sudan Ta Arewa, amma bayan rikicin daya barke a tsakanin sassan biyu, Sudan Ta Kudu ta katse jigilar cikin watan Janairun shekara ta 2012, wanda kuma Andrew Natsios, tsohon jakadan Amirka a Sudan, ya shaidawa tashar DW cewar bangarorin biyu na bukatar juna domin ci gaban tattalin arzikinsu:
Ya ce "A lokacin da aka dakatar da jigilar man fetur a tsakanin Sudan da Sudan Ta Kudu, dukkan bangarorin biyu sun yi fama da matsalar tattalin arziki, kuma ko da shike suna da tarihin gaba da juna, amma idan ba su hada kai ba, to, kuwa dukkan gwamnatocin biyu da kuma al'ummomi daga sassan biyu za su fuskanci matsananciyar rayuwa."
Tasirin katse jigilar man fetur ga kasashen biyu
Dama dakatar jigilar ta janyo hauhawan farashin kayayyaki a Sudan Ta Arewa da fiye da kaso 28 cikin 100 a shekara ta 2012, yayin da tattalin arzikinta kuwa ya sami koma baya da fiye da kaso 11 cikin 100. Ita kuwa Sudan Ta Kudu, wadda ta dogara da man fetur wajen samun kudaden shigarta, na bukatar inganta rayuwar al'ummar ta ta hanyar samar da makarantu da asibitoci da kuma hanyoyi. Kai hatta ma da batun biyan albashi kamar yanda Andrew Natsios, tsohon jakadan Amirka a Sudan, ya shaidawa tashar DW:
Ya ce " A nazarin da na yi cikin littafin da na rubuta, akwai kimanin mutane dubu 400 da gwamnatin Sudan Ta Kudu ke biyansu albashi. dubu 100 ma'aikata ne, yayin da dubu 150 kuma ke zama sojoji, kana wasu dubu 150 ke zama mayakan sa kai da gwamnati ke kula da su, kuma take kiransu a duk lokacin da bukata ta taso, kuma hanyar hana barkewar rikici a Sudan Ta Kudu itace sanya kowa da kowa cikin jerin wadanda gwamnati ke biya."
Mafita ga rikicin dake tsakanin Sudan da Sudan Ta Kudu
Yarjejeniyar da sassan biyu suka kulla a cikin watan Maris dai ba ta warware daukacin batutuwan dake ingiza rikici a tsakanin su ba, musamman batun yankin Abyei - mai arzikin man fetur, da na cancantar zama dan kasa, harma da batun kan iyaka. Lamarin da Magdi el-Gizouli, jami'i a cibiyar nazarin tafkin Rift da ke yankin na Sudan, ya ce akwai jan aiki a gaban kasashen Sudan da Sudan Ta Kudu wajen shawo kan rikicin iyakar su:
Ya ce " Wannan iyakar da suke takaddama akanta, tana da tsawo sosai, kuma mai tsarkakiyar gaske, domin kuwa ba wai kawai wurin gudanar da ayyukan soji na kasashen biyu ba ne, harma wuri ne da 'ya tawaye da ma kungiyoyin mayakan sa kai daban daban ke cin karensu babu ba, wadanda kuma suka taba nuna goyon baya ga wani bagare a lokacin da suke yakar juna."
A yanzu dai shugaba al-Bashir ya sanar da kudirin kai ziyara zuwa Sudan Ta Kudu, yayin da ita kuwa Sudan Ta Kudun ke fatan samar da bututun da jigilar man ta kasashen Kenya da Djibouti a matsayin shirin ko ta kwana don kaucewa wani rikicin da ka iya barkewa a tsakanin su nan gaba.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman