1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maslaha ta samu a tashar jirgin ruwan Sudan

Abdul-raheem Hassan MAB
November 1, 2021

Masu zanga-zangar adawa a Sudan sun janye zaman dirshan da suka yi na killace babban tashar jiragen ruwa da bututun mai na kasar da suka rufe tsawon makonni, bayan cimma yarjejeniya da dakarun kasar.

https://p.dw.com/p/42Rpo
Putsch im Sudan | General Abdel Fattah al-Burhan
Hoto: /AP/dpa/picture alliance

Masu zanga-zangar sun sake bude hanyoyin da suka hada tashar jiragen ruwa da sauran sassan kasar da suka rufe na tsawon lokaci.

Cimma yarjejeniyar na zuwa ne mako guda bayan da sojojin Sudan suka rusa gwamnatin rikon kwarya a wani juyin mulkin da aka yi Allah wadai da shi, matakin da ke barazana ga neman mafita kan halin tsadar rayuwa da al'ummar Sudan ke ciki tun kafin da kuma bayan kifar da gwamnatin tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir a shekarar 2019.