Masu gwagwarmaya na IS sun ƙwace cibiyoyin tsaro a Kobane
October 10, 2014Talla
Rahotanin daga Siriya na cewar 'yan gwagwarmaya masu yin jihadi na Ƙungiyar IS sun ƙwace iko da babbar cibiyar tsaro ta Ƙurdawa da ke a garin Kobane da ke a arewacin Siriyar kan iyaka da Turkiya.
Masu aiko da rahotannin sun ce mayaƙan na IS sun kuma mamaye manyan gine-gine na gwamnatin yankin da wata cibiya ta mayaƙan sa kai na Ƙurdawan.