Masu taro kan Iraki a Paris sun amince yaki da IS
September 15, 2014Talla
Mahalarta taron dai sun yi suna ganin cewa kungiyar ta IS wani babban kalubale ne ga kasar Iraki da ma sauran kasashen duniya baki daya, domin haka za su ba da cikekken hadin kai ga hukumomin kasar Iraki a yakin da suke da kungiyar, inda sanarwar karshen taron ta ce har ma a fannin bayar da gudumawa ta soji.
Daga nata bengare kasar Rasha ta bakin Ministan harkokin wajan kasar Sergei Lavrov, ya ce za su ba dataimako wajan yaki da 'yan kungiyar ta IS, amma kuma za su yi hakan ne, tare da zurfafa nazarinsu kan wannan lamari, inda ya ce tallafin zai je ne ga hukumomin Iraki ta yadda za su samu karfin yakar 'yan kungiyar ta IS.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo