Masu tsintar shara a Dakar
A Senegal, dubban 'yan jari bola ne ke zuwa wuri mafi girma da aka fi zubar sharar robobi da makamantansu domin yiwuwar sake alkinta su don sayerwa. Sai dai wurin na da girma daura da illa ga muhalli.
Masu neman bolar robobi da karafa
Wajen 'yan jari bola 2,000 ke aiki a wurin zubar da sharar Mbeubeuss da ke wajen babban Senegal, Dakar. Da kugiyar waya, su kan tattara sharar robobi da za a iya sabuntawa, ko konawa don samun karafa masu amfani.
Dillalan sharar da za a iya sake sabuntawa
Ma'aikatan na samun kudinsu ne daga sayer da sharar da ake iya sabuntawa wa dillalai. Wasu kan samu wajen CFA dubu 100 (Euro 150 ko Dala 180) a wata guda, a cewar kungiyar Wiego mai zaman kanta, albashi mafi kankanta a Senegal. Sai wasu 'yan jari bolar ba sa samun ya kai haka.
Warin sabbin shara
Domin samun abun kai wa bakin salati, 'yan jari bolar kan tsinci kansu cikin matsananci zafi da doyin sabbin shara a wurin zubarwar. A kullum, sai sun jira manyan motocin da ke jibge sabbin shara a tsakiyar tsaunin. Kafin su fara tsintar robobi da karafa masu amfani cikin sauri daga sharar da aka zubar.
Shanu na yawo a wurin zubar da sharar
A kowace rana, wajen manyan motoci 230 ke kawo sharar da nauyinta ya kai 1,300 a kan tsaunin. Sharar bugu da kari, na jan hankalin shanu da tsuntsaye, wadanda ke yawo a filin mai murabbin hectoci 114 domin neman abinci.
" 'Yan jari bolar sun fi asara"
Kakakin kungiyar 'yan jari bola Pape Ndiaye, ya ce rayuwa na kara tsananta a Mbeubeuss. Bayan gasar tsintar sharar, akwai matsalar farashin da dillalan sharar basa karawa. Duk da cewar aikin kare muhalli 'yan jari bolar ke yi ta hanyar sabunta sharar " a kullum su ke da asara," a hirarsa da lamfanin dillancin labaran Faransa..
Hadari ga muhalli
An san Mbeubeuss a matsayin babban haɗari ga muhalli. Lokacin da ma’aikatan suka kona sharar, hayaki mai guba yana ratsa dukkan unguwannin da mutane ke zama a kewayen. Wani tafkin da ke wajen wurin da ake zubar da sharar ya koma ja saboda gurbatar yanayi.
An kusa rufe filin zubar da sharar
Bayan watsi da Mbeubeuss na gomman shekaru, yanzu gwamnatin Senegal ta yanke shawarar rufe filin zubar da sharar. A shekarar 2025, za a mayar da ita cibiyar rarraba shara. Ga 'yan jari bolar dai, hakan tamkar kawo karshen rayuwarsu ne.