1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga sun fusata a Sudan

July 30, 2019

Jagororin zanga-zanga a Sudan, sun soke tattaunawar da aka tsara za su yi da shugabannin sojin kasar a wannan Talata sakamakon kisan yara 'yan makaranta da aka yi.

https://p.dw.com/p/3N0Oa
Äthiopien West Wellega | Treffen bezüglich Blauer Nil und Benshangul Gumuz Region
Hoto: DW/N. Dessalegn

Jagororin zanga-zangar sun ziyarci garin Al-Obeid da aka aikata kisan, ta'asar kuma da Majalisar Dinkin Duniya ta ce a yi gaggawar gudanar da bincike a kai.

A jiya Litinin ne aka kashe yaran 'yan makaranta a tsakiyar garin, kisan da masu adawa da gwamnatin suka ce na rashin imani ne.

Majalisar ta Duniya ta ce babu dalilin kashe dalibai cikin kayansu na makaranta haka kawai, tana mai cewa shekarunsu basu ma wuce 15 zuwa 17 da haihuwa ba.

Wasu ruwayoyi daga Sudan din, sun ma ce an bayar da shawarar garkame dukkanin makarantun da ke a yankin da wannan lamari ya faru.