1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga sun kutsa ma'aikatar muhalli ta Lebanon

Suleiman BabayoSeptember 1, 2015

Masu zanga-zanga sun nemi minisatn kula da muhalli na kasar ya ajiye aiki bisa yadda shara ke mamaye titunan kasar

https://p.dw.com/p/1GPc5
Libanon Protest in Beirut
Hoto: Reuters/J. Saidi

Masu zanga-zanga a kasar Lebanon sun kutsa ma'aikatar kula da muhalli da ke birnin Beirut fadar gwamnatin kasar, inda suka bukaci ministan Mohammad Machnouk da ya yi murabus, saboda takaicin da yadda shara ke ci gaba da mamaye titunan kasar.

Rashin kwashe rasha na tsawon lokaci ya zama matsala da ke tunzura al'uma bore, sannan an kwashe lokaci mai tsawo majalisar dokokin ta gaza zaben shugaban kasa. Tashin hankalin ya janyo Firaminista Tammam Salam na kasar ta Lebanon barazanar murabus, abin da zai jefa iya tabarbara siyasar kasar, wadda makwabciyarta Siriya ke cikin yakin basasa.