1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata na shirin karfafa harkokin noma a Najeriya

October 17, 2019

A yayin da ake gudanar da bikin ranar abinci ta duniya, a Tarayyar Najeriya hankali na karkata ne bisa taka rawar mata wajen bincike a harkar noma da nufin inganta sana'ar da ma wadatar da kasar da abinci.

https://p.dw.com/p/3ROFZ
DW eco@africa solarbetriebene Kühlschränke
Mata sun yi fice a harkar noma da kiwo a NajeriyaHoto: DW

Duk da cewar mafi yawan manoman Tarayyar Najeriyar da ma masu sana'ar kiwo sun kasance mata, da kyar da gumin goshi ake jin duriyarsu in ana batun ba da gudummawa ta hanyar samar da abinci. To sai dai matan sun yunkuro suna neman sauyi tare da kara neman dama da kuma taka rawa ba wai kawai cikin harkokin noman ba har ma da bincike da nufin karin daraja a tsakanin matan.

Reisanbau in Senegal
Mata na shirin bunkasa harkokin noma a NajeriyaHoto: picture alliance/Godong

Yayin wani taron kungiyar matan da ke bincike a harkar noma na shekara-shekara da aka gudanar a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar ya yanke hukuncin neman dama ta goga kafada cikin harkaar noman da bincike tsakanin mata na kasa. Dr Binta Iliyasu dai na zaman jagorar kungiyar a sashen arewacin Tarayyar Najeriyar, guda kuma a cikin jagororin taron da ke zaman irin sa na bakwai, ta kuma ce akwai fatan karfafa gwaiwar matar na iya kai wa ga kara habbaka rawar da suke takawa da ma cika burin Najeriyar da ke neman ta ci da kai ko ta halin kaka. Ko bayan wayar da kan matan da ke a cikin noman dai, babban buri na kungiyar na zaman daukakar matan Najeriyar daga masu daure awaki da tumaki a bayan daki, zuwa hamshakai na manoman da ke takama da ilimi irin na zamani.