1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata masu kwashe shara a Zimbabuwe

Aishat Bello Mahmud/YBMarch 30, 2016

Duk da cewa aikin kwashe shara da tuka manyan motoci abu ne da ke da matukar wahala a nahiyar Afrika a kasar ta Zimbabuwe mata sun himmatu.

https://p.dw.com/p/1IM9y
Zentralafrikanische Republik Wahlkampf - Anhänger Präsident N'Guendet
Mata masu kamar maza a AfirkaHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Mata a kasar Zimbabuwe sun himmatu wajen yaki da talauci ta hanyar yin kowane aiki har da aikin da ake ganin maza suka fi shahara da yin su, kamar jan manyan motoci da ma kwasar shara a cikin unguwanni da ma'aikatu a kasar.

Makanyara Gandiwa, ta fara aikin kwashe shara tun daga matakin sharar titi a shekara ta 1996, wanda yanzu likkafa ta yi gaba zuwa mai jan motar shara. Ta ce magajin garin Harare shi ne wanda ya ba ta kwarin gwiwa, lokacin wani jawabi bayan babban taron da aka yi na Beijing a 1995, inda ya karfafa gwiwar mata da su dage da yin wasu ayyukan da ake ganin na maza ne kadai.

Armut in Bulgarien
Aikin kwashe shara a bolaHoto: picture-alliance/Ton Koene

"Ina jin dadin yadda nake hidimtawa al'umma a duk sanda nake jan wannan katuwar mota, ina karfafa wa mata gwiwa da su dage su nemi na kansu ta hanyar kowane aiki ko da ma wanda ake ganin maza ne kadai ke yi, kuma yin irin wadannan ayyukan ba zai canza dabi'ar ki ba, koda ma kina da aure, za ki girmama mijin ki kamar kowa".

Duk da cewa aikin kwashe shara abu ne da ke da matukar wahala a nahiyar Afrika in an yi la'akari da yadda ake amfani da karfi ta hanyar daga kugiya da saukewa da ma kwasar sharar, Magareta Magore ta kwashe tsahon shekaru shida tana wannan aiki ta bayyana kalubalen da ta fuskanta.

"Mun fuskanci matsalolin da suka shafi lafiya da fari, kamar hawan jini da tsananin gajiya amma yanzu ya zama labari don nasaba na kan tashi tun karfe hudu na asuba na fita aiki kuma ina jin yadda magidanta ke yaba aikin da muke yi, suna cewa mun fi maza yin aiki mai kyau da juriya don su koyaushe suna aiki cikin hanzari".

Videostill vom DW Video Gabun: Making money with waste
Sarrafa shara dan neman kudiHoto: DW

Zimbabuwe ta samu ci-gaba kwarai ta fannin bai wa mata aiki, amma duk da haka kungiyoyin kare hakin bil Adama a kasar na ganin cewa ana bukatar a kara ba wa mata dama in anyi la'akari da yadda maza su kai kaka-gida da dukiyar kasar.