An fara ba wa mata lasisin tukin mota a Saudiyya
June 4, 2018Talla
Gwamnatin kasar Saudiyya ta fara rabawa mata lasisin tukin mota kamar yadda babbar kafar yada labaran kasar ta sanar a wannan Litinin.
Sanarwar ta kara da cewar a halin yanzu hukumar kula da ababen hawa a kasar ta fara maye gurbin shaidar tukin da ta amince da ita a baya da lasisin tuki duk dai a cikin shirye-shiryen bai wa matan kasar izinin tuka mota wanda za a kaddamar a ranar 24 ga watan Yunin wannan shekara.
Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin kasar ta Saudiyya da mata za su fara tuka mota bayan fara halartar filayen wasan motsa jiki tun bayan bijiro da sabbin canje-canje da Yarima Muhammad bin Salman ya fara gudanarwa.