SiyasaJamus
An tsaurara matakai a Sudan bisa fargabar zanga-zanga
November 13, 2021Talla
An kara karfafa matakan tsaro a manyan biranen Sudan a yayin da ake dakon gagarumar zanga-zangar ta masu rajin kare gwamnatin farar hula da sojoji suka kifar
Manyan kasashe masu karfin fada a ji na cigaba da bayyana matukar damuwa kan turka-turkar siyasar ta Sudan, da ma sabuwar majalisar gudanarwa da jagoran juyin mulkin kasar Sudan ya kafa.
Kasashen Amirka da Birtaniya da Norway da kungiyar Tarayyar Turai da kuma Switzerland, sun yi kira ga jami'an tsaron kasar ta Sudan da su bayar da damar fadin albarkacin baki ba tare da fargaba ba ga 'yan kasar, gabanin zanga-zangar ta masu rajin kare mulkin farar hula.
Tuni mahkuntan na Khartoum suka sanar da rufe dukkan gadojin da suka ratsa Kogin Nilu gabanin zanga-zangar ta wannan Asabar.