Matan Najeriya sun shiga tsaka mai wuya a Saudiyya
September 26, 2012Hukumomin Saudi Arabiya na cigaba da tsare mahajatta mata daga Najeriya a filayen jiragen Jedda da Madina.Matan sun gudanar da wata zanga-zangar lumana domin tilasta ma hukumomin ƙasar Saudiya yanke hukunci akan makomarsu.
Har yanzu hukumomin na Saudia basu ce ma matan su fiye da ɗari 900 ufan.
Tun kammala sallar subahin ta safiyar Laraba ne maniyatan mata 'yan Najeriya dake tsare a hannun hukumomi Saudiya a filin jirgin saman Jedda suka gudanar da wata zanga-zanga ta lumana, inda suke neman bayani akan makomar niyar su ta aikin hajji daga hukumomin. Wanda bayan ɗaukar lokaci jami'an ƙasar ta Saudia suka lallashi matan su fiye da 900 da su basu awowi biyar za su ji sakamako, to har yanzu bata canza zane ba.
Na tuntuɓi wata daga cikin matan dake tsare ta wayar salula wadda tace har yanzu hukumomin na Saudia basu ce uffan ba:
Wannna lamarin ya shiga kwana na biyar da soma tsare maniyata aikin hajji mata, daga BNajeriya sabili da rashin mazajensu ko muharrammansu a tafiyarsu ta aikin hajji, kuma malam Yusuf Yahaya Alibawa, na daga cikin waɗanda suke ta ƙoƙarin gayawa hukumomin Najeriya halin da ake ciki.
Wasu maniyata da suka zo sane da irin matsalolin da sauran mata a Najeriya suka faɗa sun yi ƙoƙarin ceto wasu, amma duk da hakak wasu da yawa na cigaba da shiga hannun hukumomin Saudiya.
Tuni sauran maniyata daga johihi da dama na Najeriya suka cigaba da bayyana damuwarsu akan wannna lamari.
Mawallafi: Aminu Abdullahi
Edita: Yahouza Sadissou Madobi