Bijere wa dokar hana fita a Sudan
April 12, 2019A kasar Sudan bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir karkashin jagoranmcinministan tsaro Awad Ibnouf, har yanzu masu zanga-zanga na nuna kafewarsu na ganin an dora kasar kan tafarkin dimukuradiyya. Duk ma da dokar hana yawon dare da sojojin suka kafa, sai da aka samu wadanda suka toshe kunnensu suka fita.
Har zuwa karfe goma na dare a kasar ta Sudan, masu zanga-zangar daga zaune sun ci gaba da zaman dirshen inda suke ci gaba da kiran neman ganin dorewar dimukuradiyyar da ma al'ummomi na kasa da kasa suka rika neman ganin ta wanzu. Zaman kuwa na zuwa duk da gargadin da sojojin suka yi na cewa kada masu zanga-zangar su kuskura su ki mutunta dokar hana fitar daren.
Mahukuntan birnin Washington na Amirka sun yi kira ga sojojin kasar da su yi taka tsantsan tare da ba wa fararen hula damarsu ta shiga a fafata da su a harkokin mulki.