1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasa sun kalubalanci dattawa kan muhalli

Yusuf Bala Nayaya
November 7, 2017

Sophie Kivlehan, da tawagarta ta matasa kimanin 20 masu shekaru daga 10 zuwa 21 a wani bangaren na taron duniya kan muhalli a birnin Bonn ta ce gwamnatin Amirka ta ci zarafinsu kan sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/2nBDB
UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn Proteste
Hoto: DW/K. Wecker

Yayin da aka shiga rana ta biyu na taron sauyin yanayi mai lakabin Fiji COP 23, da ke wakana a birnin Bonn na Tarayyar Jamus cikin mahalartansa da ke zama har da manyan gobe, wata matashiya mai kimanin shekaru 18 jika ga sanannen masani a fannin sauyin yanayi kuma dan fafutikar kare muhalli a Amirka James Hansen ta nuna bacin ranta ga dattawa da ke da shekaru a duniya kan tsare-tsare da suka yi kan muhalli, kuma ta ce za ta gurfanar da gwamnatin Amirka a gaban kotu.

Sophie Kivlehan, da tawagarta ta matasa kimanin 20 masu shekaru daga 10 zuwa 21 a wani bangaren na taron na duniya kan muhalli a birnin Bonn ta ce gwamnatin ta Amirka cikin tsare-tsarenta da suka shafi sauyin yanayi ta ci zarafin manyan na gobe ga take hakki da kundin tsarin kasa ya basu da 'yanci na rayuwa da walwala da ma muhalli da suke rayuwa a cikinsa.

Babban burin da Kivlehan ke da shi dai shi ne na ganin kotu ta tilasta gwamnati daukar matakan da suka dace wajen kare muhalli musamman ganin yadda gwamnatin Shugaba Trump ke nuna halin ko'in kula. Irin wannan fafutika dai na nan ta matasa a kasashe inda suke fatan ganin gwamnatoci sun kyautata makomarsu ta fiskar muhalli.