1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

A Senegal matasa sun rungumi sana'o'in zamani

Abdoulaye Mamane Amadou
November 17, 2021

Matasa da dama na yankin Kazamans na Senegal sun rungumi sana'o'in dogaro da kai dan debewa kansu takaici da magance zaman kashe wando da ake fuskanta a wannan yankin na kudancin Senegal.

https://p.dw.com/p/436Fe
Dakar, Senegal, Arbeitslosigkeit
Hoto: DW/J. von Mirbach

Matasa da dama na yankin Kazamans na Senegal sun rungumi sana'o'in dogaro da kai dan debewa kansu takaici da magance zaman kashe wando da ake fuskanta a wannan yankin na kudancin Senegal. Wasu daga cikin sana'o'in da matasan suka runguma har da kwasan shara a gidajen jama'a, lamarin da masu sana'ar suka ce suna samun kudaden da ke biyawa kansu wasu bukatu na yau da kullum.

An dauki dogon lokaci ba a ga tarin tulin sharar da ake jibgewa kan hanyoyi da dama ba a binrin Ziguinchor, tun bayan da matasan wani kamfani mai suna GIE "Vision futur'' suka rungumi sana'ar ta kwasar shara ga iyalan da suke da bukatar haka a cikin farashi mai rahusa.

Da misalin sefa 1500 katankwacin euro biyu da rabi ko dalar Amirka uku, matasan kan kwashe sharar gidajen jama'a sau biyu a mako tare wanda hakan ke taimawa wajen tsaftace birnin da ya sake samun fasali.

Asusun raya kasashe na kasar Jamus GIZ ne dai ya tallafa wa matasan wajen kafa wannan masana'antar, inda ta ware masu kudade da suka kai kimanin miliyan 32 dan sayen kayayakin aikin kwasan saharar da suka hada da babura masu kafafu uku da kwandon aje shara akan hanyoyi da gidaje a wani yunkuri na ganin cewar matsalar ta kau a birnin na kudancin Senegal.

Kamfanin ya dauki matasa fiye da 70 aiki, ya kuma kafa wata cibiyar da ke kuka da tattara sharan da ake daukowa daga gidaje dan inganta su da kuma duba yiwuwar sarrafa sharan zuwa wani abun da ka iya amfanin jama'a, sai dai wannan na a matsayin wani mataki ne da kamfanin matasan ke son cimma a gaba.

Babban burin matasan a yanzu shi ne na ganin sun tabbatar da ingantacciyar tsafta ga birnin na Ziguinchor  har ma da sauran biranen da ke makwaftaka da karamar hukumar.

Da dama dai daga cikin al'ummar yankin na unguwanni dabam-daban irinsu Grand-Dakar na yi wa matasan san barka, duba da yadda sannu a hankali suka raba su da tarin tulin shara da ta dabaibayesu. Wasu da dama dai a unguwannin birnin irinu Souleymane Diédhiou na masu ganin yanada muhimmanci mahukuntan birnin Ziguinchor su bayar da cikakkiyar kulawa ga wannan kamfanin na kwasan shara, a wani mataki na kara inganta rayuwar al'umma da tsaftace birnin, duba da yadda hakan ya zamewa hukumomin birnin wani karfen kwafa a baya, lamarin da ya sha haifar da cece-kuce tsakanusu da al'umma.