1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matatar man fetur ta Warri a Najeriya ta dawo aiki

December 30, 2024

Matatar man fetur ta Warri da ke yankin Niger Delta a Najeriya ta dawo aiki gadan-gadan bayan shafe sama da shekaru 10 a rufe.

https://p.dw.com/p/4ohCl
Guda daga cikin matatar man fetur na Nigeria a Kaduna.
Guda daga cikin matatar man fetur na Nigeria a Kaduna.Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Shugaban kamfanin NNPCL na Najeriya  Mele Kyari ya ce duk da cewa matatar man ta Warri ta fara aiki amma ba su cimma kashi 100 cikin 100 na yadda suke son matatar ta gudanar da aikinta ba.

A wata sanarwa da babban mashawarcin fadar shugaban Najeriyar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce an rufe matatar man wanda ke fitar da ganga 125,000 a kowacce rana a 2025, sakamakon lalacewar wasu daga cikin injinan matatar da kuma karancin gurbataccen man da za a sarrafa, inda a yanzu aka kammala kashi 60%.

Karin bayani: Kamfanin NNPC ne zai sayar da man matatar Dangote a Najeriya

Jihohi hudu ne suka yi hadaka wajen samar da gangar man fetur 445,000 a kowacce rana a Najeriya, ciki har da ta jihar Kaduna da ke arewacin kasar wacce ke samar da ganga 110,000 a kowacce rana.

Karin bayani: NNPCL ya fara dakon mai daga matatar Dangote

Matakin gwamnatin Najeriyar na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin man fetur na attajirin Afirka Dangote ya fara samar da ganga 650,000 a kowacce rana.