1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar gurbacewar muhalli a arewa maso gabashin kasar Sin

November 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvJW

Ana kara fuskantar gurbacewar muhalli a yankin arewa maso gabashin kasar China. A halin da ake ciki hukumar birnin Charbarowski dake yankin kan iyakar Rasha da China ta yi shailar kafa dokar ta baci. A wannan yankin kogin Songhua da ya gurbace sakamakon malalar sinadari Benzin mai tattare da guba ya hadu da na Amur. Kamfanin dillancin labarun Rasha Itar-Tass ya rawaito cewar a ranar daya ga watan desamban ruwan dauke da gubar ta Benzin zai kai birnin na Chabarowski. A halin da ake ciki ruwan gubar ya kai birnin Harbin mai miliyoyin mazauna a cikin China. A ranar laraba da ta wuce hukumomi suka hana yin amfani da ruwan kogin Songhua. Ruwan kogin ya gurbace ne sakamakon malalar guba bayan fashewar wasu abubuwa a wata masana´antar harhada magunguna kimanin makonni biyu da suka wuce.