A duk safiya daga gida Abdel-Wahab Taya kan yi jigila a kekensa. Shi dai dan tireda ne da ke cin kasuwa a tsaunukan Nuba a Sudan. Yana tafiyar kwana biyu domin sayo ganyen shayin Kofee ko lemo a yankuna da ke da matukar hadari a duniya tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.