Matsalar rikicin filayen noma a Tanzaniya
January 13, 2018Talla
Rikicin filayen dai ya shafi wajen heka 4000 na noma da ke kusa da babban gandun dajin nan na kasar da ke Serengeti, inda al'ummar yankin ke rikici kan filayen tare da gundumomin Bunda, Butiama, da kuma Serengetin wanda ko a watan Nuwamba da ya gabata, sai da wata tawaga ta gwamnatin kasar ta Tanzaniya ta je yankin domin neman magance rikicin.
A jiya Jumma'a ne dai rikicin da ya barke ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da aka kashe ta hanyar saransu da adduna yayin da suke aiki a cikin gonakinsu da ke cikin gundumar Serengeti, inda aka ce wadanda suka kai harin 'yan wani gari ne na gundumar Bunda a cewar Jarafi Mohamed shugaban 'yan sandan yankin, wanda ya tabbatar da kama mutanen 40 da ake zargi sannan ya ce suna ci gaba da neman wasu.