Matsalar 'yan ci-rani a ƙashen Larabawa
November 10, 2013'Yan sanda a Saudiyya sun yi arangama da baƙi yan ci-rani a Riyad babban birnin ƙasar. 'Yan ci-ranin dai sun bada kai ne ga 'yan sanda, bayan mummunan tarzuma tsakaninsu da ya kai ga mutuwar muta ne. Dama tun daren jiya Asabar ne dai jami'an tsaro su ka yi wa baƙin zobe, a wani gidan da suka taru. A ziyar da ya kai birnin Makka wakilinmu Ado Abdullahi Hazzad, ya ji ta bakin wasu baƙin 'yan Najeriya da Nijar, inda wasu su ka soki rashin kulawa da baƙi na ofisoshin jakadancin ƙasashen. A fadar daya daga mutannen da ya zanta da su, ya sha zuwa ofishin jakadanci don a sake masa takardu, amma jami'an ba su taimaka masa ba. A yanzu haka dai 'yan sandan Saudiyya na loda mutanen cikin safa, zuwa wasu wuraren da aka kebe don tsare baƙin, kafin a mai da su ƙasashensu na asali.
Haka lamarin ya ke a Katar (Qatar)
Babban jami'in MDD da ke kula da kare yancin dan Adam, ya buƙaci hukumomin ƙasar Katar da su, inganta yanayin dakunan kwanan baƙi 'yan ci-rani da ke ayyukan gine-gine a ƙasar. Jami'in wanda ya ganewa idanunsa inda baƙin ke kwana, ya ce wasu dakunan tamkar bukkoki ne. Akasarin baƙin dai na aikin gina filayen wasannin ƙwallon ƙafa da ƙasar ke shirin daukar nauyin gasar cin kofin a shekara ta 2022. Kungiyoyin kare yancin dan Adam, sun dade da kiraye-kiraye ga ƙasashen yankin Gulf, su inganta kula da yancin baƙi 'yan ci-rani. 'Yar mitsitsiyar daular Katar, ta yi mugun suna wajen rashin mutunta haƙin baƙi 'yan ci-rani.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu