1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na karuwa a Nijar

Salissou BoukariJune 7, 2016

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHCR, ta sanar da cewa a kalla mutane dubu 50 ne suka bar matsugunnansu daga yankin Bosso na Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/1J1uM
Bruno Geddo UNHCR
Bruno Geddo na hukumar UNHCRHoto: picture-alliance/dpa/G.Vanden Wijngaert

Hakan dai ya biyo bayan harin da 'yan Boko Haram suka kai a ranar Juma'ar da ta gabata a garin na Bosso da ke cikin jihar Diffa. Mafiyawan wadannan mutane sun yi gudun hijiran ne da kafafunsu har ya zuwa sansanin 'yan gudun hijira na Toumour da ke da nisan kilomita 30 da yammacin garin na Bosso, a cewar Adrian Edwards mai magana da yawun hukumar ta UNCHCR, yayin taron manema labarai da ya gudanar a birnin Geneva.

Mista Edwards ya ce mutanen na rayuwa ne a filin Allah kuma suna bukatar babban taimako, sannan wasu sun gudu zuwa birnin Diffa da ke da nisan kilomita 140 da garin na Bosso, yayin da wasu suka nufi garin Kabalewa da ke Arewacin Bosson, inda a nan ma ake da wani sansanin 'yan gudun hijirar da ke iya daukar mutane 10,000 wanda shi ma a halin yanzu yake daf da cika makil.

Harin na Bosso dai ya kasance mafi muni da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai, tun bayan da kasar ta shiga cikin wannan yaki gadan-gadan a watan Fabarairu na shekara ta 2015.