1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki na ci gaba da dai-daita Sudan ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afarOctober 23, 2015

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa dubban mutane a kasar Sudan ta Kud ka iya fuskantar matsalar yunwa da za ta yi ajalinsu.

https://p.dw.com/p/1Gsz0
Karancin abinci a Sudan ta Kudu
Karancin abinci a Sudan ta KuduHoto: Getty Images/AFP/N. Sobecki

Kungiyar Samar da Abinci ta Majalisar Dikin Duniyar FAO da Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara wato UNICEF da kuma Shirin Samar da Abinci na Duniya WFP ne suka yi wannan gargadi inda suka ce a yanzu mutane 30,000 ne ke fuskantar matsanannciyar matsalar rashin abinci a kasar. Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya fi shafar jihar Unity da ke arewacin kasar sakamakon fadan da ake ci gaba da gwabzawa a yankin, wanda ya sanaya kungiyoyin agaji suka ce ba za su iya kai kayan agaji ga al'ummar yankin ba. Sudan ta Kudu ta samu kanta cikin halin tasku tun bayan da rikicin kabilanci ya barke tsakanin dakarun sojojin kasar da ke goyon bayan Shugaba Salva Kiir da kuma wandanda ke marawa tsohon mataimakinsa Riek Machar baya, rikicin kuma da ya rikide zuwa yakin basasa.