1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa ta yi muni a Zimbabuwe

Columbus Mavhunga/Usman Shehu UsmanMarch 16, 2016

Hukumar abinci da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa yanzu haka a fadin duniya ana fuskantar karancin abinci a sassa daban-daban.

https://p.dw.com/p/1IE2D
Simbabwe Nahrungsmittelhilfe
Hoto: Privilege Musvanhiri

A kasar Zimbabuwe matsalar rashin abinci sai kara muni take yi, inda yanzu haka mutane kimanin milyan hudu ke bukatar tallafin abinci. Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana cewa dubban daruruwan yara ke bukatar magani cikin gaggawa. Hukumar kula da abinci ta duniya FAO ta shirya wani taron bita kan matsalar a kasar ta Zimbabuwe.

Fari da yankin gabashin Afirka ya yi fama da shi dai na cikin abin da ke sa lamarin karancin abinci ke mumanan a Zimbabuwe, inda yanzu haka akasarin jama'a da ke zama karkara ke fuskantar yunwa. Chimimba David Phiri jagoran hukumar abinci ta duniya a yankin kudancin Afirka, ya ce lamarin ya yi muni.

Simbabwe Dürre Hilfslieferung
Hoto: picture alliance/dpa/T. Mukwazhi

A cewar hukumar ta abinci da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa yanzu haka a fadin duniya ana fuskantar karancin abinci, biyo bayan rashin yin girbi mai kyau a kasashen kudancin Afirka, domin haka gudanar da taron ke da muhimmanci, musamman a kasar da ke fama da matsalar kamar Zimbabuwe, inda mutane milyan hudu ke matukar bukatar agajin abinci. Prisca Mupfumira ita ce ministar kula da kula da jin dadin jama'ar Zimbabwe, kuma su ne suka yi rigista na mutanen da suke bukatar abinci bayan shugaban kasar Robert Mugabe ya kafa dokar ta-baci bisa lamarin na yunwa.

Simbabwe Dürre Hilfslieferungen
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Bayan da kasar Zimbabwe ta yi shelar shiga bala'in yunwa, Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu ta tara dala miliyan 80 domin takaita bala'in. Kasar Zimbabwe dai daya ce kawai cikin kasashen kudancin Afirka da ke fama da karancin abinci. Domin a farkon bana Firaminista Hailemariam Desalegn kasar Habasha ya yi shelar neman agajin sama da dala milyan 10 kan agajin abinci.