1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun cin hanci na sahun gaba a yakin neman zabe a Brazil

Suleiman Babayo Thomas Milz (daga Rio)
October 2, 2018

Tsarin dimukuradiyya ya gamu da matsalolin rashin yarda daga jama'a, a Brazil matsalolin cin hanci da rashawa da ake bankadowa tun shekara ta 2014 musamman a kamfanin man fetur na kasar sun kara sukurkuta batun.

https://p.dw.com/p/35rXU
Brasilien Sao Paulo - Demonstration für Jair Bolsonaro
Hoto: Imago/Zuma Press/C. Faga

Za a iya cewa kusan duk manyan jam'iyyun siyasa na kasar ta Brazil na cikin matsalolin na cin hanci da rashawa da aka bankado. Kashi 68 cikin 100 na 'yan kasar sun nuna rashin yarda ga jam'iyyun siyasa na kasar inda wani binciken ke cewa adadin ya kai kashi 87 cikin 100 a binciken wata cibiya. Masana suna gani wannan shi ne abin da ake tsammani ya zama martani mutane inda haka ke taka rawa wajen rashin iya magance matsalolin da suka yi wa kasar katutu a cewar masanin siyasa Carlos Perreira da ke wata cibiya a birnin Rio de Janeiro:

Brasilien Sao Paulo - Demonstration für Jair Bolsonaro
Hoto: Imago/Zuma Press/C. Faga

"Tunanin cewa 'yan siyasa daya ne kuma cin hanci na kawo matsaloli ga dimukuradiyya, ya kai ga imanin rashin iya amfani da dimukuradiyya domin magance matsalolin al'uma."

Brasilien Proteste in Rio de Janeiro
Hoto: Reuters/F. Texeira

Rashin yarda tsakanin masu kada kuri'a da 'yan siyasa ba sabon abu ba ne, amma badakalar da aka bankado a kamfanin man fetur na kasar ya kara dagula lamarin. Lokacin da Brazil ke karkashin gwamnatin kama karya tsakanin 1964 zuwa 1985 wannan rashin yarda ya fito kiri-kiri. Yanzu dai Jair Bolsonaro ake ganin zai iya lashe zaben Brazil na ranar 7 ga wannan wata na Oktoba, tun lokacin da aka soke takarar tsohon Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva.

A cewar masani dokoki Michael Freitas Mohallem yana ganin babu yadda za a yi dan takara Jair Bolsonaro ya raba kansa da abin da ke faruwa kamar yadda yake ikirari:

"Manyan jam'iyyu sun gaza sake sabunta masu rike da manyan mukamai na jam'iyyun. Kuma maganar samu wani sabon jini ya gaza samuwa. Bolsonaro wanda yake ikirarin sabon jini ne, shi kansa ya shafe shekaru ana damawa da shi a harkokin siyasa."

Daga cikin 'yan majalisa 513 da aka zaba a shekara ta 2014, 36 ne kacal suka samu kuri'un da ake bukata sauran sun samu bisa tsarin Brazil cewa idan dan takara ya samu fiye da kuri'un da yake bukata sai jam'iyyarsa ta yi amfani da kuri'un wajen ceton wasu 'yan takara. Daya daga cikin 'yan takara a jam'iyyar ma'aikata Tatiana Rogue daga Rio de Janeiro tana cikin wadanda suka amfana da tsarin:

"Tsarin wanda ya dace ne. Jam'iyyu suna takara bisa hakidu. Idan mutum ya kada kuri'a ga dan takara, haka ya zama kai tsaye ga hakidar wannan dan takara."

Brasilien Sao Paulo - Demonstration für Jair Bolsonaro
Hoto: Imago/Zuma Press/C. Faga

Bisa tsarin na Brazil sabon zuwa majalisa na bukatar kimanin kuri'u 116,000 sannan mai neman sake dawowa na bukatar kimanin kuri'u 766,000 inda gabilin kudaden yaki neman zaben suke salwanta.