Matafiya kan fuskanci matsaloli a Afirka ta Yamma
October 27, 2021
Wannan dai haifar da tambayoyin na tasirin shige da ficen kasashen da suka amince a yi zirga-zirga ba tare da takardar izinin shiga kasa da ake kira visa ba tsakanin kasashe da ke cikin Kungiyar ECOWAS.
Manufar shige da fice marar shinge da kasashen yammacin nahiyar Afirka su ka cimma yarjejeniyar samar tsakanin kasashen ECOWAS shi ne habaka kasuwanci da zamunta domin karfafa tattalin arzikin kasa na wadan nan kasashe da ke cikin kungiyar
To sai a iya cewa Haka ba ta cimma ruwa ba don kuwa matafiya na samun tarnaki tsakanin kasashen saboda zargin cin hanci da ake zargin ana samun tsakanin jami'an da ke kula da shige da fice da kuma na Kwastam har ma da jami'an Soji da ‘Yan Sanda da ke kada shingen bincike a yawancin hanyoyin.
Wasu matafiya a wadan hanyoyin da na tattauana da su sun bayyana min cewa an karbi kudade daga hannun su a irin wadan wurare da sunan biyan kudin shiga kasa da ya kama daga Jaka 10 ko kuma Naira dubu 10 ko kasa da haka ko ma fiye a wasu wurare.
Da farko na jin ta bakin Malam Hidir Ahmad Musa dan jihar Kano a Najeriya wanda kuma shafe shekaru ya bin hanyoyin tsakanin kasashen yammacin nahiyar Afirka ya ce suna ganin matsaloli na karbar cin hanci tsakani jami'an da ke kula da iyakokin kasashen.
A matsalolin da ake gamuwa da su ba a ware mata domin kuwa Sayyada Rabi Bababa daga jihar Gombe a Najeriya ta ganin sai mahukuntan sun tashi tsaye domin magance matsalolin.
Harkokin kasuwanci na shiga mawuyacin hali tsakanin kasashen musamman ganin yadda ‘yan kasashen ke fama da biyan kudade na ba gaira ba dalili a hanyoyin da suke bi.
Ko me ya kamata a yi amgance wannan matsalar Malam Usman wanda aka fi sani da Ladan daga Niamey a jamhuriyar Nijar ya bani amsar wannan tambaya.
Masana da masharhanta na bayyana fargabar wannan matsala da ake za iya samun sauki safarar haramtattun makamai da kuma ruruwan wurar rikicin matsalolion tsaro saboda an fi kulawa da karbar kudi maimakon abun da mutum yake wucewa da shi.