Bore ya jawo sakin dan fafutika a Aljeriya
May 31, 2019Talla
Mahukuntan kasar Aljeriya sun saki dan fafutikar nan Aouf Hadj bayan kwashe watanni uku a gidan kaso kamar yadda lauyansa ya bayyana a wannan Juma'a. An dai saki Hadj, dan shekaru 49, daga gidan kaso na lardin kudancin Ghardia a ranar Alhamis kamar yadda lauya Salah Dabou ya bayyana a shafin Facebook.
Sakin nasa dai na zuwa kwanaki bayan da abokin gwagwarmayarsa Kameleddine Fekhar ya rasu a gidan kaso sakamakon yajin kin cin abinci. Lamarin da ya jawo zanga-zanga da ma tofin alatsine na 'yan fafutika.
Dukkaninsu dai Fekhar da Hadj an kama su a watan Maris saboda sukar mahukunta ciki har da sojoji kamar yadda 'yan fafutika suka bayyana.