Mawuyacin halin 'yan gudun hijira a Kenya
May 2, 2017‘Yan gudun hijran da ke tserewa rikicin kasar Sudan ta Kudu na ci gaba da mamaye yankin Kakuma da ke kasar Kenya, inda a yanzu ake da sansanin ‘yan hijira na biyu mafi girma a kasar. Sai dai yanzu hankali ya soma tashi kan yadda barazanar fari ke mamaye wajen da kuma zaman 'yan gudun na hijira.
Wata Alice Maraka da iyalanta baki daya na wannan yanki na Kakuma. Daga wajen da suke a yanzu, sai da ta dauke su tafiya mai nisar gaske kafin su isa wani wajen da suke yiwo iccen da suke Konawa don samun gawayin amfani.
Lokacin da sanyi ke tsanani, Alice na sayar da gawayin da take yiwowa a sansanin ‘yan hijira da majalisar dinkin duniya ta samar a Kakuman, don amfani da abin da take samu wajen samun abinci.
A cewar ta, tasa guda ta gawayin na sama mata awo biyu na maiwa ko wake da suke amfani da su. Alice dai ‘yar asalin wata al'umma ce da ake kira Tukana, wata kabilar da ke arewa maso gabashin kasar Kenya.
Asalinsu dai makiyaya ne da suka dogara da amfanin da suke samu daga dabbobinsu. Wasun su kuma suna harkar tufafi.
A halin da ake ciki, bala'in fari ya kashe masu dabbobi masu yawa, da kuma ya jefa rayuwa cikin garari, abin ma da ta sanya su cikin harkar ta gawayi.
Aikin na su na gawayi dai aiki ne da ke haddasa barazana ga muhalli saboda sare itatutuwa da suke yi, da kuma masana suka ce shi ma daya daga manyan dalilan da suke janyo fari.
Majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin agaji dai na samar da tallafi ga kimanin mutane dubu 180 da ke sansanin Kakuma, yayin da ita kuwa gwamnatin kasar Kenya ke daukar nauyin mazauna Turkana.
Wata matsalar ita ce ta sabanin da ake samu tsakanin al'umomin biyu da ke amfani da wasu wuraren samun ruwan sha, musamman ma da farin ke kara tsanani.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana kokarin samo maslaha ga wannan rigimar da bangarorin biyu ke ciki. Sai dai akwai wadanda ke ganin wuyar hakan, ganin an sami bayanan cewa, wasu mazauna Turkana, sun dakatar da hatta ma'aikatan hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya dammar debo ruwa, yayin da suka ziyarci wajen a baya-bayan nan.