Mayakan IS na dab da kwace Kobani
October 7, 2014Turkiya ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bada duk wata gudun mawa da ta dace a yakin da ake da kungiyar mayakan IS, bisa sharadin cewa al'ummomin kasa da kasa za su samar da wani tsari na hadin gwaiwa da zai kai ga karshen gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na kasar Siriya a cewar Firayin Minista Ahmet Davutoglu.
A wata ganawa da manema labarai, bayan tambayarsa ko kasar ta Siriya za ta tura da dakarunta a wannan yaki da mayakan IS. Davutoglu ya ce idan har sauran kasashe za su bada ta su gudunmawa a wannan fannin kasar ta Turkiya ma za ta yi hakan.
Ya ce samar da wani tsari na hadin gwiwa da zai kawo karshen gwamnatin shugaba Assad ba wai kawai kungiyar IS ba, shi ne zai kai ga samun nasarar kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar ta Siriya.
A makon jiya ne dai majalisar dokokin kasar bayan kada kuria, mafiya rinjaye na mambobin majalisar suka amince da shigar rundinar mayakan sojin kasar wajen fatattakar mayakan na IS, amma ba a ganin sojan kasar a wurin duk kuwa da cewa masu jihadin sun shiga garin Kobane da ke a kan iyaka da kasar ta Turkiya.
Shi kuwa a nasa bangaren shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyar a ranar Talatannan ya bayyana cewa garin na Kobani na dab da fadawa hannu masu jihadin inda ya ce dole se an samar da dakarun sojan kasa kafin a kai ga nasarar murkushe mayakan na IS.